Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link

Sharhin Littattafai: Rich Dad Poor Dad By Robert T. Kiyosaki

 

Bangon Littafin - www.saninkai.com


Littafin a cikin Jumloli Uku

  1. Littafin Rich Dad Poor Dad yana magana ne game da Robert Kiyosaki da iyayensa maza guda biyu— mahaifinsa, wanda ya haifeshi wanda yake kira da 'Poor Dad' (Ma'ana "Talakan Baba"), da kuma mahaifin babban amininsa, wanda yake shi kuma mai arzikine — kuma yana kiransa da 'Rich Dad' (Ma'ana "Baba Mai Arziki")  ya nuna yadda tunanin iyayen nasa biyu suka taka muhimmiyar rawa wajan kallon da yakamata yay wa kuɗi da kuma juya su ta hanyar saka hannun jari.
  2. Kana iya zama mai arziki ba tare da samun manyan kudaden shiga ba.
  3. Masu arziki suna sa kudi su masu aiki kuma suka nemo musu wasu kudin


Muhimman Al'amura Guda Biyar

  1. Talakawa da masu matsagaitan hali sunayin aiki ne domin kudi (Aikin Albashi). Su kuwa masu kudi suna sa sanya kudi domin samin kudade
  2. Abin da ke da mahimmanci ba shine yawan kuɗin da kuke samu ba. Abu mai mahimmanci shine ya ka kula dasu.
  3. Masu arziki suna tara dukiya ne. Masu matsakaitan hali da talakawa kuwa sai siyan abubuwan da ba  wajibai ba waɗanda suke yi wa kuskure kallo a matsayin kadara.
  4. Gogewarka da kudi shine abinda kai da kudin da ka samu, yadda ka kashesu ko kuma ka adana su, zubasu inda zasu sake kawo wasun su, da kuma sarrafasu ta yadda zasu jima ba tare da an musu kashewar lokaci daya, kasa kudin aikin nemo ma wasu kudin wanna shine gogewa akan sha anin kudi.
  5. Babbar kadarar mai karfin tasirin da muke da ita shine Fikirar da Tunanin mu


Muhimman Darussa Daga Littafin "Rich Dad Poor Dad"

  • Darasi na Farko: Su Masu Kudi Basa Aiki Don Kudi Kawai 
  • Darasi na Na Biyu: Mai Yasa Ake Koya Ilmin Sanin Kudi
  • Darasi na Uku: Ka Damu Da Abinda Ya Shafeka
  • Darasi na Hudu: Tarihin Taxes Da Kuma Tasirin Kamfani
  • Darasi na Biyar: Masu Kudine Suka Kirkiri Kudi
  • Darasi na Shida: Kayi Aiki Domin Koyo - Kada Aiki Don Kudin Kwadago

Rairayar Littafin "Rich Dad Poor Dad"


“Akwai banbance tsakanin talauci da tabarbarewa ko kuma rashin  kudi a hannu, karyewar kudi, karanci ko rashin su a hannu abune na wucin gadi, shi kuwa talauci abune na har abada.”

“Kudi yana zuwa yana kuma tafiya, amma idan kana da ilimin yadda yake aiki, za ka iya sarrafa shi kuma ta hakan ka fara tara dukiya.”

Tsoro da kwadayi su ne manyan abubuwa biyun da ke tafiyar da rayuwar mutane har abada.
Akwai mutane da yawa da ke da'awar cewa ba su da sha'awar kuɗi. Koyaya, za su sanya awanni takwas a rana a wurin aiki.

Akwai mutane da yawa da ke da'awar cewa ba su da sha'awar kuɗi., su basa san kudi, him amma kuma a hakan suke, bata awanni takwas a rana a wurin aiki.

"Yaudarar kai ne tunanin cewa aikin albashi garkuwa ne ga rayuwar dan Adam kuma ma wai tsaro ne "

"Fikira itace ke sa asami maganin matsaloli kuma a warwareta, wanda hakan shine mabudin sirrin samun dukiya"

Wajibi ne a gareka da kasan banbanci dake tsakanin 'Asset' (Kadarar dake kawo kudi) da kuma 'Liabilities' (Kadarar Da Akewa Dawainiyar Kashe Kudi)

Ita kadara mai kawo kudi saka kudi take a aljihunka, ita kuma kadarar da akewa dawainiya fitar da kudi take daga aljihunka

Tushen matsalolin kuɗi shine jahilci, a cikin duka ilmin kalmomin na rubutun bayanai dana kididdigar lambobi.


"Kudi sau da yawa yana bayyana wa a fili aibi na ɗan adam, yana sanya haske kan abin da ba mu sani ba.".



Tsabar kudin da ake juyawa na bayyana salon takun sarrafa kuɗin mutum.



"Yawancin mutane basu san cewa suna fama ne da matsalar rashin kudi adalilin rashin fahimtar yadda ake juya kudade da sarrafa su"



"Babban Abunda yake yashe kudaden wasu mutane shine haraji."



Yawam kudaden shiga na nufin yawan haraji. wannan shi ake kira da  "Bracket creep" (Ma'ana idan kana samin kudi da yawa tom zaka bada haraji da yawa, iadan ka kara samu zaka kara bada haraji)

Post a Comment