Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link

Mikakkiyar Hanya Zuwa Ga Cimma Nasara

Hanya zuwa ga cimma nasara ba mikakkiya bace, hanyace mai dauke da guguwar iska wanda juriya tareda gyara domin samun daidaito yazam wajibi domin samun damar cigaba da tafiya zuwa tabbatacciyar hanyar daza ta mika mutum zuwa ga karshen matakin cimma muradi. Yazama kamar wajibi ko tilas musani cewa inda ace samun cimma nasara abune mai sauki da kowa zaiyi domin kusan kowa yana fadin cewa yana so, ko kuma yana sha awa. Saidai furta ana so ko muradi ba mallakar hakan bane domin tabbas ana bukatar zunzurutun aiki domin samun abinda akace ana so din. Aiki kusan shine abu can gaba da yake nuni da cewa mutum da gaske yake domin haka shi yasa kullum marubuta musamman na fannin karfafa gwiwa suke ta nanata shi ba dare ba rana. Duk wani abu da mutum yakasance yanaso a al adar duniyar nan yanda aka shimfidata to tilasa ne da ka tashi ko kitashi ki ne meshi, idan ilmi ne a je a koyeshi, idan sana a ce itama aje a iya, idan kudi ne shima sai ai abunda akasan yana sawa asami kudi ta hanyar yi n bincike da kuma dogon tunani. Gano yadda ake abu tare da jurewa wajan aiwatar da abinda aka koya ko aka gano shine ake kira da aiki. Don haka karanta littafi na iya zama aiki, nanata karatu na iya zama aiki, yin hidima na iya zama aiki da zai kai mutum da samun abunda yakeso.

Cikin wannan articles din za ai bayani kan wasu matakai guda goma na hanya zuwa ga cimma nasara.


1. Rubutattun Muradai

Dola ne yazam kana da buri/muradi domin ka tsaya akan hukuncin da ka dauka a rayuwarka sannan ka sanarda da hankalin ka da tunaninka kan abunda zaka nufa. Karfin tasirin dake tattare da Rubattatun Muradai abune da mutane kadan suka taba amfani dashi. Matakin farko a hanyar cimma muradi shine rubuta abinda kake so na taikatatcen zango da kuna na dogon zango a dukkanin bangarorin rayuwarka:. Kamar misali Lafiya, Alaka, Kudi, Yakin, sannan dama Aikinka . Bazaka iya fara tafiyaba ba tare da taswirar inda kake nufin zuwa ba.



2. Kwaikwayon Nasara

Domin cimma nasara dolene kana bukatar wadanda zaka dinga kwaikwaya wanda tuni sunyi abinda kake so kayi, ka duba ta yadda suka kai ga ci, abunda sukayi, irin abubuwa da suka karanta, kasadar da suka dauka, tsarin da sukai amfani dashi kuma suka bi. Dole sai kai duba ga kaidojon da kuma yanayin cimma nasararsu. Yi amfani dasu amtsayin abin kwaikwayon ka domin da wanda yafika ko ya huce ka dashine zaka dinga koyi domin shio ya je inda ake so a riska, don haka shine zai zama madubin ka. Kafin ka afka cikin harkar da kake so kai nasara akai yana da kyau kai duba yawan aiki da ake bukta domin cimma nasara, yarda da faduwa , juriya, naci, kin sarewa jajircewa duka suna cikin abunda ake bukata akan ko wane muradi da ake so a cimma sabida haka yana da kyau ka tambayi kanka cewa shin zaka iya tsayawa duk wannan ka shirya fuskantar duka wadannan abubuwa, yana da kyau da kasan a hasashen ka irin  lokacin da kake da bukata da kuma lokacin da wasu kafinka suka shafe kafin zuwa matakin da suke domin babu gajeriyar hanya wanjan cimma nasara dole sai anbi kaidoji, sannan sai ka auna shikuma abinda za a samu a matsayin sakamako idan ya cancanci ai mai duk wannan tom babu shakka saika apka in kuwa bai can canta ba saikai tunani akai kasake lazum abun domin gano wani abun da yasa kake ganin bai cancantaba idan babu to yafi kyau daka barshi.


3. Kirga Farashi

Bayan ka fahimci abinda zesa ka cimma nasararka. wanda ya hadamma lokaci, aiki, karfi, himma, ilmi, harma da irin kasadar da zakai. To yakamata da kasan farashin ka, kafin ka fara. kAsan irin girmna sakamakon da kaima zaka samu bayan yin duk wannan aikin, ka lissafa farashin da nasara zata baka hakan zai baka damar kasancewa da kuma tabbatuwa akain abinda kakeyi . Hakan zai taimaka kwarai wajan samun kwarin gwiwa tareda hangen nasararar wanda zaizam danba agareka. Sannan kafin kamayi nisa a ciki ya kamata da kasan cewa dolane kazam cikin shirin biyan dukkanin farashin da yakamata domin cimma nasara. Wanann ya hada da duk wahala tsanani ko radadi da zaka gamu dashi a halin tafiya, don sanin hakan na da muhimmanci sosaita yadda ma idan baza ka iyaba ma ana bazaka iya jurewa ba to kada ka wahalar da kanka kawai wajan farawa, gwara  kaje ka nemo wani abun daban wanda da zaka iya biyan farashinsa, wanda zaka iya jurewa duk wanann, domin babu amfani cewa nima na gwada amma kuma banyi nasara ba ko ban kai ga ciba, ko abin bai yuhuba, dayin hakan gwara gano hakan tunda farkon farko amatsayinka na dan Adam mai hikima da basira.


4. Kirkirar Tsari

 Kana Bukatar tsararren tsari wanda zai kusantaka ga muradinka a kowace rana. Me kake bukatar yi kullum domin ya kara kusantaka ga cimma muradinka? Me  yakamata ka karanata? Wa zaka karanta? Taya zaka habaka kasuwancin ka? Ka habaka Sana arka? Ka karfafa sanayya? Da kuma aikin ka? ko ka bayyana ta wasu hanyoyi, gurare da rukunai ko yayane. Kaifin hankalin ka da tunani shike kaiwa ga cikar babban buri idan aka sami dorewa akai. Babu wani abu daza yi shi cikin kwarewa ko asami nasara akai batare da an anyi masa ingantaccen tsari ba. Tsari shine babban sinadarin aiwatar da ko wane abu a muhallin sa kuma alokacin da ya dace. A sabida haka yakamata da kasami tasri mai kyau domin samun sakamok mai kyau.



5. Kayi Aiki Tukuru

 Ko wace rana dolane kai aikin da nasarar ka ke bukata domin ta kusanta  da cikar burunka. Wannan shine abu mai wahala da yake kawo karshen tafiyar mutane da yawa ta cikar muradansu. Aiki shine abunda yaraba muradi da kuma abunda son sa  kawai ake, shi ya banbata shi da fata samu, da kuma mafarki. Aiki shine abin nufi da sanya  himma domin gudanar da duk wani abu da ake bukata domin ya kusantaka da  kusanta  ta kurkusa da cikar buri a kowace rana. Yakamata musani cewa dan da da akwai sauki kowa da kowa zai iya. Harda nasara yadda take da dadi da sanya farin ciki tana sauki koda rabin misalin haka da ba shakka kowa ya cimma mata. Domin babu cikakken mutum mai hankalin da baya son yay nasara. KOWA yana so sai dai kadanne suke iya jurewa sharadan samunta wanda sune kuma ake kira da masu nasara, sudun ba wai na daban bane a sufa ko halitta kawai sun tsaida tunanin sun akan cewa komai yakama zasuyi asara waduwa, rashin biyan bukata da sauran duka kalubalen da ka iya zuwa ayayin da suke gwagwar maya sam baze dakatar da suba sun yarda da su jure wannan rashin jin dadin na wani lokaci domin samun farin ciki agaba.



6. Aiki da Kwakwalwa

Aiki kadai bashine ba, Yin aikin daya dace shine abinda yafi kuma shine ma yakamata. Yanada da kyau ace akwai wani bayanai da zai baka damar ganin abinda zai matsar dakai kusa zuwa ga burinka, domin tantance wanda baya kusantaka da burinka da wanda ma baya aiki kwata kawata. Da wanda yake bata ma lokacin ka da karfi. Dolane ka dinga bibiyar cigban da kasamu tare da yin kiddiddiga domin ganin aikin da yake da amfani da ma ana. 80% na dukkan sakamakon na iya zuwane daga kashi 20% na aikin ka, tom in hakanta faru saika ninka aikin da yakasance yana baka sakamako mai kyau  wanda baya bayarwa kuma ka share shi.



7. Kididdigar Bayanai


 Yana da kyau ace ka karanci yadda masu irin harkar ka suke, me sukai amfani dashi  yay musu aiki?, me ce ce  babbar nasarar su da faduwa?, taya suka cimma mata?. Babu lokacinda tarihi bai bada bayanai akan abubuwan da sukai aiki ko wadan da basu aikin ba akowane fanni ka masana anta. Don haka tarihin nasarar rar wasu ya zma kamar littafin kwaikwayo a gareka domin ta hakan nne zaka iya gane , irin shirin da zakai domin cimma nasara a rayuwar ka, kai daga nai kasn basu bacci yadda kowa yake yiba, don haka kaima se kai duba domin gyara abibiwan da yakasance kowa da kowa yake yi. ba wai zaka galla zawa kanka bane, a a kawai zakai abinda ba kowane yake yiba domin zama na daban domin wani mai iya magana yace "idan kanasan sakamako na daban to kaima fa wajibine kai abu na daban wanda ba ka taba ba. Film din Moneyball bababn shirine wanda yake koya yadda akae kididddiga  da afmani da bayanai wajan inganta kimar kudi da kuma lokaci.





8. Karko Da Muhimmanci


 A kome kake dolane sai ka kirkiri sannan ka dabbakar da samar da abu mai karko da kuma kima a idon jama a domin samun nasara. Dolane kabayar da mai yawa ga abokanan cinikin ka, masu biye dakai, dalibai, ko kuma a duk alakarka, sama a yadda kake dauka daga garesu. Ko a abu buri ma idana mukai duba buri na kashin kai kwai domin cimma masa kana bukatar ingataccen abinci, ingataccen tunani, da ingataccen atisaye domin cimma muradin kyakkyawar lafiya. Sannan farsahin da kake biya dolane ya kere kimar abinda kake son samu. Farashin da kake nema agurin mutane dolane yay kasa da abinda kake bayarwa. Idan kayanka ya zama a banza babu wani abu da yake da amfani a kasuwancin., shi yasa da ace waduwar kasuwan ci zata zo yazam to cewa babu kimar kimar kasuwanci aciki, tofa alaka da  abokan kasuwanci, kwarin gwiwar ma aikata, da abokanan huldar ciniki duka zasu sanfene domin nema wasu daman makin da sukafi musu.



9. Yanayin Tunani:

 Tunani mai kyau da kuma dabi a shike zama kaifinka, Tunani marasa kyau zai iya zuke karfinka. Idan har baka yadda da kan kaba da kuma muradunka to waye wanda zaiyi? habbakakken tunani bashine yake bada tabbacin samun nasara ba domin kasancewr akwai sauraran sababai, amma kuwa tabbas tunanin rashin nasara ya kusata da ya zama tabbacin ta. Don haka mukasance masu yiwa kanmu zaton alkairi, kyakkyawan zato na nufin babban alkairi wanda samunsa yakusata ga mai yin sa. kazamto mai fadawa kanka zantuka na gaskiya kuma na alkairi domin hakan na zama allaura gareka da jikinka kan taimaakon wajan aikata alkairi da samunsa. Tunanain rashin sa a nada tasirin da zai iya tsaida ka wajan samun biyan bukatarka, yana sawa mutum ya gaza yarda da kansa balllantana baun da yakeyi, yana kashewa mutyum gwiwar jurewa tareda saurin sarewa, haka zalika yana hana samun nasarar tunda dama ba ayarda da za a cimmata mata, yana hana godewa yar karamar nasara da akai samu tareda hangen nasama wanda suka dauki lokaci mai yawa suma kafin saukai ga inda suke, yana hana girma dimin baze bari mutum yasamu damar kaiwa ga ci ba tunda baze iya jurewa jarrabobin rayuwa ba wanda zasu sa ya goge kuma ya zauna akaai daram. 




10. Juriya

 Sarewa tabbaci ce na rashin nasara, cigaba da gwadawa hasashene na iya cimma nasara. idan dai har kana kan tafarkin dai-dai to neman cimma burin burinka ba tareda tsayawa ba zai cigabane  daga karfin yakinin hasashenka zuwa ga matakin nasara har sai yakai 100% wata rana. babban raunin mu shine Sarewa. " Babbar hanyar cimma nasara akullum shine sake gwadawa sake gwadawa."  Thomas Edison 

Kada mu sare! Kada mu Daina! Kada mu hakura! Kada mu janye! Kada u juya Baya! Kada Mu rage girman burin mu! Kara Girman aiki kawai muke bukata! Komai mai yuwuwane idan har mun yarda da hakan! Rashin samun abinda ake so a tayin farko baya nuna cewa wai bazamu samu ba har abada! Hakan wata hanyace ta jarabta domin mu nuna yadda muke so abin shin zamu sake nema? mun shorya da gaske muna son abun? zamu iya jurewa? babban abun ma shine mun cancanta damu samu abun? jurewar mu itace take nuna dukkanin amsoshin wadannan tambayoyi domin ba a bukatar amsa irin ta baki domin kowama eh zece amma kwa ta wannan sigar tabbas aikin kane zai nuna eh din ka ko a a.

Ya mai karanta wanann articles din a wannan shafin na  WWW.SANINKAI.COM nasani ka/ki nada muradai, burika da kuke so ku cimawa tabbas akwai su dayawa nasan wannan, tam tambayar anan itace waca amsa kuka bayar cikin zabuka guda biyu da rayuwa ke bayarwa EH ko A A. yi comments a kasa domin sauran alumma suji karfin ra ayinka da kuma gogewarka tareda bamu takaitaccen bayani akan dalilin da yasaka kai/ki kai wannan zabi. IDAN KUMA BAKI/KA  gane abunda nake fada ba to tabbasa ba a fahimci wannan articles ba don haka da bukatar sake nananta karantawa tin daga farko da budadden tunani tayihu idan aka sake din a fahimta.

"Idan Har kasan Inda zaka akan hanyar ka ta cimma nasara, kuma ka cigaba da tafiya akan tafarkin da ya dace, Lokacine kawai tsakanika da muradinka"

Post a Comment