Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link

Halaye 11 Domin Cimma Gagarumar Nasara Arayuwa

 


  Shin ka kunsan me ke sawa wasu mutane suke zama na daban acikin al-umma? Kun San kuwa waca dabi ace mafi mahimmanci domin samun daukaka a rayuwa? Ku kun san dalilin da yasa wasu manyan mutane ke dadewa zamani yana tafiya dasu, sabanin wasu da suke yin gajeran zango? Waca sifa irin wadannan mutane keda ita Da suke zama na daban cikin Mutane? Amsoshin wadannan tambayoyi tabbas sun ta allaqa ga wasu kyawawan dabiu tare da halayya wanda ke teamakawa wajan cimma wannan nasarar. Domin ko ba a fada maka ba, babu yadda za ai wanda yayi aiki tukuru ya hana kansa bacci ya jajirce ya jure duk wasu jarrabawa da kunci na rayuwa domin cimma burinsa, yayi dai-dai da wannan yake wasa, bacci, kawace-kawace tare da burika marasa kan gado (Domin babu wani tafarki da akabi domin cikar muradin) Su sami sakamako iri daya da wancan na Farkon.

Kwarai babu shakka akwai wasu kebantattun halaye wanda ke maida mutum gama gari zuwa na musamman, sannan daga na musamman zuwa mai Karfafa Gwiwa ma'ana masu rainon mutane zuwa matakin cimma muradan su. Tabbas yayin da ka fahimci wadannan halaye kuma ka zartar dasu a aikace to babu shakka zaka budewa kanka wasu  boyayyun tasirin da kake dauke dashi, na samin damar kaiwa ga cimma nasara da samun daukaka a rayuwarka.

Na rairayo wadanann ingantattun Halaye, Tare da Dabaru harma da Fasahohi wanda zasu taimaka matuaka wajan zama na daban kuma na musamman. Domin Inganta rayuwa da samun sa ada acikin ta.

1. Ka Zama Mai Tashi Da Wuri


Tashi da wuri na da matukar mahimmanci, domin a lokacin ruhin dan adam yake madaukakin mataki yin tsaftacaccen tunani harma da fikira. Domin kwakwalwa lokacin a wanke take tas babu wasu sauran abubuwa da aka sa mata. Kamar Dai Sabon Memory Wanda sam ba shirgin komi acikinsa. Da Safiyane zaka sami cikakkiyar kwanciyar hankali da nutsuwa. Domin babu wani abu daze janye ma hankali, saboda haka zaka sami damar maida hankali akan koma mai kasa gaba. Wannan yanayi yana bada damar tsara abubuwan da kake so ka gudanar a wannan rana tare da lokacin da kake so kai harma da lokacin da ka ware domin gudanarwar. 

2. Yin Atisaye Akai-akai

Ka kasance mai motsa jiki akai- akai. Ka ware wani lokaci na yin atisaye; zaka iya zuwa gidan motsa jiki, ko yin sassarfa, ko kuma wani dan aikin mosta jikin domin bawa jiki dama na ya konar da sinadarin kuloris don ingatta jiki da kara mishi karfi. Hakan zai karawa jikinka inganci da lafiya wanda zai taimaka matuka wajan  yin tunani mai kyau tareda samar da sabbin tunani wajan warware matsala ko kawo cigaba a cikin al umma. Yin Atisaye akai akai yana bada muhimmiyar gudummawa na cin abu mai kyau: Motsawar gabbai cikin kyan yanayi: sannan yana kawo samun bacci mai dadi.
Wadannan abubuwa guda uku manyan alamomine na cikakkakiyar lafiya, ka maisheda lokacin ka wajan kare lafiyar jikinka, domin idan kana da lafiyar jiki zaka iya fuskantar duk wani kalubalen rayuwa kuma a karshe ka fita daga ciki  kayi

3. Kabi Muradin Zuciyarka

Yana da matukar mahimmanci ka muradin ka sannan kabishi shi wannan abun da kake so. Abun takaici, wasu mutane sukan bi muradan da ba nasu ba, abunda bashi suke so ba, suna bin muradan wasu kuma akarshe sai su mummunar waduwa. Ya zama wajibi agareka da ka gano Karfinka da hurumunka, ka muhimmanta karfinka damin tabbatar da hurumun abunda ya shafi rayuwarka domin cimma gagarumar nasara a rayuwa. Muradinka shine abinda yakamata ka bibiya kada kabi muradin wani, sannan kada ka yarda wani yace ma ga abinda zakai ko ga abinda zaka iya kawai domin bashine yayi ka ba don wannan hurumine na ubangijinka. Muradin ka shine babban makamin kaiwa ga cimma kololuwar nasara sabida san da kake masa.

Idan kabi muradin ka ta hanyar dorashi akan baiwar da Allah yayi maka, bazaka lura da ya ka karar da lokacin ka ba ko rayuwar ka. Domin aikin ka baze taba ginsarka ba hartakai daka ji ma wai aiki kake, domin zai zama abin ban'awa gareka wanda hakan zaisa ka kware kuma kayishi cikin kwarewa iyawa tare da gogewa. Wasu mutanen sukan wa kudi hankaro maimakon bin mafarkin su wanda a karshe sai kaga sun gaji da abinda sukeyi kawai domin kudin badan suna soba ko ya dace da baiwarsu. Magana ta gaskiya itace idan kabi muradin rayuwarka topa ba shakka kudin zai biyoka kai tsaye. Domin kwarewar ka a muradinka zai sa kowa yace sai kai wanda nasan kunsan mai hakan yake nufi. 

4. Ka Nemi Dabi'A

Domin a karni na Ashirin, anyi bincike da yawa akan mutanen da suka ci nasara a rayuwa domin gano menene musabbabin nasaral









Post a Comment