Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link

Zuwa ga Matasan Arewa (Karanta Mai Yuwa Ya Sauya Rayuwarka)


Daga Alkalamin Likitan Sana'A


Kamar yadda dayawa daga cikin masu tsiyarar wannan shafin namu mai suna SaninKai wanda yake ta kokkari wajan kawo muhimman bayanai a al'amura wanda uska shafi neman ingannta rayuwar dan Adam zuwa matakin cigaba da kuma nasara, wanda muke taba bangarori da dama, yau mun zo muku da wani muhimman bayani akan wani fasihi kuma ma abocin sani a sha ani na sana a da kuma kasuwanci, wanda daga jin sunan sa ma kasan ba wasa. "Likitan Sana a" Bussiness Consultant ne kuma yanayi Radio Program a tashoshi da dama a jahar Kano dake Nijeriya, kuma insha Allah zamu cigaba da bibiyar sa a shafikansa domin rairayo muku abubuwan ilmin sana o i da yake koyarwa. Haka zalika kuma zaku iya danna wannan link din domin shiga shafinsa na facebook kaitsaye.

A cikin wani bayani da liktan sana a yayi yayi bayani wanda a 'title' na rubutun ya sa masa taken "Zuwa Ga Matasan Arewa" ga cikakken bayanin nan a kasa. Tare da sharhi domin karin haske ga masu karatu.

BAYANAN LIKITAN SANA A ZUWA GA YAN AREWA

Daga cikin irin wayewar da ku ke buƙata a yau akwai sanin Yadda Za Ku Gamsar da Wanda Zai Ba Ku Jari domin samun damar cin gajiyar samun rancen kuɗi ko talkafin kuɗi kyauta don fara yin sana'a ko bunƙasa wadda ku ke yi.

A matsayina na wanda ya taɓa cin gasar kasuwanci ta ƙasa wanda na taɓa tsallake matakai guda uku na tantancewa kuma a ƙarshe na fuskanci alƙalai guda uku don gamsar da su na cancanta a bani kyautar kuɗi a Youwin Programme kuma ƙwararren mai bawa ƙanana da matsakaitan sana'o'i shawara akan yadda ake fara, gina da kuma bunƙasa kasuwanci yau zan nunawa ƴan uwana matasa yadda ake gamsar da wanda zai ba da jari (rance ko kyauta).

Hanyoyin da za ka bi don saurin gamsar da wanda zai ba ka jari su ne;

1. Matsalar da ka gano (problem). 



Duk wata sana'a da ka ɗaura aniyar yi matsala ce ka gano za ka warwarewa mutane. Ana buƙatar ka yi taƙaitaccen bayani akan irin matsalar da yadda ta ke damun mutane. Idan kana da wasu alƙaluma da za ka yi togaciya da su ana buƙatar ka kawo su.

Abun nufi anan shine kwarararrun yan kasuwa (Enterpreneurs) sa sauran masana ilmin kasuwanci sun tattara bayanan ma anar kasuwanci cikn jumulolin "warware matsalar masu nemam maganin matsalar su" san samu anemi matsalar da take ciwa mutane tuwo a akwarya wacca ta damesu, tom sai a kirkiro maganin matsalar, to wannan shine sana ar maganin daze warwareta din ta yuhu kayane, ko kuma aiki, ko ma dai makamantansu. Duk wani kasuwanci a duniya abunda yake yi kenan kuma wannan shine ginshikin sanin me kake so kayi ma ana kaima sana ar ka waca irin matsala zata warware? ga mutane masu neman biyan bukata (consumers). Bara in kara baku miasali domin saukin fahimta: Kamfanin Google ya warware matsalar nema cikin sauki wato (search) kusan kome kake nema a internet zaka sameshi a google domin zasu hadaka wanda yake da abunda kake nema ta hanyar baka  addreshin sa na yanar gizo domin zuwa shafinsa ta yuhu littafi kake nema,hoto,waka a sauransu. Kamfanin Amazon shi kuma ya warware matsalar mutane ne ta hanyar kawo hanya mai sauki da zakai saye da sayarwa kana kwance a dakin ka. Kamfanin Facebook sun saukaka hanyar sadara ga alummar duniya, MTN sun saukake wa mutane matsala ne ta hanyar bada dama ta yin waya komi nisan zango. Wannan shine irin matsalar da wadanann kamfanunuwa suka warwarewa duniya ba ma al umma kawai ba. Al amarinsu yayi girman da matsalar duniya suka warware kamar yadda Elon Musk ya samar da kamfanin Tesla wanda yake jigilar yan sama jannati zuwa jan sarararin samaniya duniyar wata da sauran makalukati dake sama. 

Irin wannan shine abunda ake bukata da sana arka ta bada amsar irin matsalar da zata warwarewa mutane. Ba lalle ne saika fara da manyan abubuwa ba domin hakan na faruwane a hankali ta hanyar jajircewa tareda aiki tukuru. Komai girma ko kankancin kasuwancin da kake so kai yana da kyau da ka bada masar matsalar da sana arka zata warware.


2. Mafitar da ka samar (solution). 



Anan ana so ka faiyace a taƙaice hanyar da za ka bi don warware waccan matsalar da ka zaiyana. Wannan shi ne ke tabbatar da cewa ka na da ilimi, ƙwarewa ko fasaha ta samar da mafita akan waccan matsalar.

Abun da likitan sana a yake nufi anan shine kawo gasassun bayanai akan hanyoyin da zaka bi dom magance ita matsalar da sana ar taka da kazaba zatai. Wannan shine mataki na biyu da yazam wajibi kayi bayani akai. Wannan ilmin ka da kake da shi gogewa da kuma dabara wacca ka koya a rayuwa ta hanyoyi da dama, wanda ta hakane kadai za a gane ko kagane. Domin idan muka duba kusan manyan sana o i na yau da kullum da aka fara zakuga cewa akwai mutane dayawa da za a iya cewa kai tsaye iri daya suke, kamar misali acan sama kamfanin Amazon daya saukake hanyar cinkayya ta hanyar maida ita yanar gizo akwai wasu manyan kamfanunuwa na duniya da suma suka warware kwatankwacin irin wannan matsala alal misal, Alibaba, WallMart, da sauransu akwai dubban su sunana wasu sunkai a kirga dasu wasuma sun durkushe kafin ma asansu. To wannan na nuna cewa akwai lalle hanyar da kowana kamfani kebi ko kuma mai sana a domin warware al ummma matsala. Wannan tsarin ko hanyar da zaka bi itace sirrin ka da kuma garkuwarka itace damar da zata baka dama idan kune kuka fara kirkirar sana ar, mutane su sami biyan bukata da wannan hanya domin magance matsalar su wacca ta ke damunsu, idan kuma bakune kuka fara ba to sai kuzo da sabon yanayin da wanda sukeyi kafin ku su basayi, wannan shine zai sa ku zama na daban, ta hanyar zuwa da wasu mafitar da ba a warware taba, ko kuma inganta hanyar ta hanyar zuwa da sabon yanayi domin kara  samar da karin gamsar da alumma. 

3. Matsayin Kasuwar Da Damanmakin Da ke Cikin Ta. 

  



4. Waɗanda ke cikin kasuwar (competition). 



Anan kuma ana so ka kawo misalai na mutanen da basu gaza uku ba waɗanda ke yin irin sana'ar kuma suke samun cigaba. Duk wanda ya gaza kawo wannan kamar ya na nuna cewa bai san waɗanda ke yin sana'ar ba kuma da ainihin yadda ake yinta.

Wanann ma wani ginshikine mai matukar amfani da yakamata asani gabanin fara sana a, mutane nawane keyin irin sana ar da za a fara domin hausawa nacewa daga na gaba ake gane zurfin ruwa, yana da kyau a auna cigaban da san ar keda shi ta bangaren wanda sukeyin irin sana ar; anan akwai fashin baki ba wai karfin ikon kashe kudine na mai sana a bane ke nuna gwabi ko albarka da ke cikin sana a, duda cewa eh hakan ma na daga ciki amma akaso mai yawa akwai mutanen da keyin sana a amma sakamakon basu iya sarrafa kudi ba sai su zama kamar bama sa samu daga sana ar wanda anan kunga lafin daga masu yin sana ar ne ba daga ita sana ar ba. Wasu lokutan kuma yanayin yadda ake gudanar da sana ar ne yake bukatar gyara, anan kunga sabon tunani ne ake bukata domin ingatta sana ar domin ta dinga bada riba mai yawa. Muje zuwa nagaba


5. Yadda za ka bambanta na ka (competitive advantage).



 Anan kuma ana son ka zaiyana hanyoyi uku cikin abinda bai wuce saɗara ɗai-ɗai ba ka baiyana yadda za ka inganta ta ka sana'ar don ta banbanta da waɗancan mutum uku ko kamfanoni uku da ka zaiyana a sama. Ka tabbatar ka fitar da yadda za ka ƙarawa ta ka sana'ar daraja.

Anan kusan cigaban sharhi nasamane wanda yake magana akan manyan abokanan sana an=rka wanda suma wani ginshikine na nemo inda kamata ka kawo gyara da sauyi. Tunani mai zurfi ake bukata anan yanada kyau ai dogon nazari akan wannan nukda domin anan samin nasararka take, maimaita abu kan yadda aka sabayi gaba daya babu fikira aciki don haka kana baukatar zuwa da sabon tunai domin kara gamsar da alumma akan ita sana ar.


6. Nawa za ka siyar (price).



 Ana buƙatar ka faɗi nawa za ka ke siyar da hajar ko kuma nawa za a ke biyan ka kuɗin aiki.

Bayan an kammala duk wannan saikai duba da nawa yakamata ka sayar da hajarka da kake so ka dinga sayarwa, in kuma aiki nme kakeyi nawa yakamata ka karba. Anan ma ana bukatar da ai duba sosai ta hanyar bincike mai zurfi a wuraren mutanen da suke irin wannan sana a, domin sanin yadda suke siyarwa ko karba nada mahimmanci kwarai da gaske wajan yanke farashin ka kaima. Anan kanan da zabi guda biyu kodai ka kara farashi sama da yadda sauran mutanen ke karba domin nunawa mutane cewa lallai naka yafi karko da kyau da ingacacci wanda hakan na dauke da kasada: na farko mutane kullum so suke su sayi abu da sauki a farsahin da zasu iya saya kuma don haka wannan dokar ta economics tana da wuyar sha ani ta yadda zai yi wuya ka iya samin nasarar siyar da hajarka wacca akwai irinta kuma a farashin dayafi naka sauki, amma kwarai idan dai har ingaccin yakai kuma na gaske ne to tabbas za aci nasara kuma dadin dadawa ga karin riba mai yawa amma fa sai an tabbatar da an bada gamsuwa fiyeda ta wancan hajar domin cimma wannan aiki. Sai nabiyu shi kuma shine karyar da farashin kayan domin janyo hanakalin mutane ta hanyar ribatar wannan dokar ta economics: shima wannan zabin nada nasa hatsarin domin kuwa idan ba a lissafa kudaden kashewa ba na samar da hajar idan kayane bayan cire dukkanin farashi domin gujewa matsalar yin babbar asarar da za a iya rasa uwa da riba idan ba ai taka tsantsan ba.


7. Da suwa za ka yi aiki (team). 



Anan kuma ana son ka baiyana waɗanda za ka gudanar da sana'ar ka tare da su tare da nuna irin yadda ƙwarewarsu, iliminsu da gogewasu za su cicciɓa sana'ar ka zuwa matakin cigaba.

Team sune mutanen da za  ai akin tare dasu abokanan aiki nada tsairi matuka wajan cigaban ko wana irin kasuwanci saboda haka zabinsu abune da sai anyi la akari da abubuwan da shi kasuwancin ke bukata wanda aka zaba, domin da sune ake iya cimma duk wata nasara ko akasan haka


8. Hanyoyi da za ka ke samun kuɗi a kasuwancin (revenue streams). 

Anan abinda ake buƙata shi ne ka yi bayanin hanyoyin da zaka ke samun kuɗin shiga. Misali idan wanki da guga ne za ka ke samun kuɗi na wanki, guga, guga mai sitati da kuma aikn gaggawa (express). Wanda bai san hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na sana'ar sa ba bai shirya ba.


9. Nawa za ka ke samu a wata ko shekara (revenue projection). 

Anan ana so ka ƙiyasta abin da za ka ke samu duk wata wanda in ka tattara zai ba ka damar sanin abinda za ka samu a shekara guda. Hakan na da muhimmaci domin idan rance ne za a baka ta nan za a san cewa za ka iya biya akan lokaci ko kuma ba za ka iya ba.


10. Nawa ka ke bukata da yadda za ka kashe wajen farawa (request)

 Anan ana buƙatar ka faɗi adadin kuɗin da zai ishe ka fara sana'ar. Sannan ka faɗi hanyoyin da za ka bi wajen yin amfani da kuɗin misali kama haya, siyan kayan aiki, biyan albashi, kuɗin wuta, kuɗin zirga-zirga da sauran su.


Duk wannan abubuwan za ka iya rubuta su a abinda bai fi shafi ɗaya ba ko biyu. Ka tabbatar duk abinda za ka rubuta ya zamto mai ma'ana. Akwai abinda ake kira One Page Business Plan wanda irin wannan jawabin ne a shafi guda ɗaya tal ake yi wanda duk lokacin da ake buƙatar ka tura da idea ɗin ka ka za ka aika shi ba tare da ɓata lokaci ba. Idan an gamsu da abinda ka rubuta ana tambayar cikakken bayani ko business plan wanda shi kuma za ka zauna ka faɗaɗa wannan taƙaitaccen.

Game sharhi karin bayani ko kuma tsokaci koma gyara zai iyayi a comments box dake kasa. Idan ma babu zamuso kai koda fatan alkairi ne domin kara mana karfin gwiwa.

Wannan bayanan sun fito ne daga alkalamin Likitan Sana'A wanda wanann shafi na saninkai yayi sharhin wasu daga cikin jerin abubuwan da marubucin ya lissafo domin zama kamar fashin baki da kuma bude bayannan a zayyane domin samun karin fahimta. Kuma zaku iya bda guddumawar ku, rubutun ku ko wani abu daze taimaki al umma domin dorawa a wanann shafin mai albarka ta hanyar turowa ta email akan email din mu na saninkai2836@gmail.com. mun gode

Post a Comment