Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Test link

Acewar Warren Buffett; Abubuwa Uku (3) Ne Suka Banbanta Masu Aiki, Ma Abota Cin Nasara Daga Masu Mafarkin Gaibu

Gabatarwa

Warren Buffett ya kasance sannan attajirine domin yana daga cikin mutane d dole seka sa dasu idan ana maganar manyan masu kudi na duniya shine shugaban kamfanin Berkshire Hathaway wana kusan kamfanunuwa goma sha biyar ke karkashinsa, haka zalika yana da hannun jari a manyan gammayar kamfanonin yan jari hujja irin su Coca Cola, Bank Of America da Apple.

Yanzu da yake a shekarar sa ta 90, Oracle of Omaha wanda wannan kamar sunan da al ummarsa suka sa masa ne sakamkon shi mazaunin Omaha ne wanda mutane ke bin tafarkin salon kasuwancin na iya juya kudi da saka hannun jari a inda ya dace. A cikin wannan article din zamuji yadda ya bayyana mahimman darusan daya koya a rayuwarsa 

Kwarai babu shakka cewa Buffett shine wanda mafi kwarewa a iya saka hannun jari the Oracle of Omaha, kamar yadda aka sani. yafara saka hannun jari ne tun a shekarar 1942 da kudi kimanin $114.75 wanda kuma yanzu yana daga ciki mutane goma dasuka fi kowa kudi a fadin duniya Baki Daya

Duda cewa ana ganin sa a matsayin mai kuskure a a sha ani na ilmin tsumi da tanadi wato Economics ( wanda babban kuskuren sa da yay shine zuba zunzurutun kudade da yay kusan kimanin $358 million a US Airways.), domin kusan wannan kuskuren ne mayasa aka san shi a duniya wanda yazama mafi shaharan kuskure a duniya wanda ake bada labari domin yazama izina ga mutane wanda suke da sha awar zuba hannun jari. Kamar dai wadannan darussa guda uku dake kasa wanda ke da matukar muhimmanci in ka karanta da ka dabbakar dasu a rayuwar ka domin samun sakamako mai kyau


1.Kaso Aikin Ka Kake

  Abu mai sauki wanann ai, domin idan kai abunda kake so, kabi muradin ranka aikin ka yakasance ya fito ne daga fannin da kake so kake bada himmarka to nasara ce zata biyo baya, Buffett yayi rayuwa ne a gwadaben wannan ka idar, yayi jawabi kan cewa, "Idan kana jin dadin aikin da kake, bazaka taba yin aiki ba, a ga dayan rayuwarka." ya rufe da cewa "lokaci ya riskeka wanda yakamata kafara abinda kake so. ka zabi aikin da kake so. Idan kasamu nasarar yin hakan, tom fa zakai tsalle ne daga kan gadon ka da safiya cikin shaukin zuwa aiwatar dashi." To abun tambayar anan shine menene kake matukar so da gaske? Menene kakeyi don jin dadin yi kakeji kamar ma ba aiki kakeba? tom wannan shi yakamata ka gano da kanka domin kafi kowa sanin kanka.


2. Kadena Ta adar nan ta "Tsotsar Hannu"

Ka taba zama ka shafe a wanni masu yawa domin yanke hukunci akan wani abu karshe ka tashi ba tare da kayi wani abu akaiba, duda cewa ya kamata da kai hakan? wannan, a ganin Buffett, shi ya kira da "Tsotsar hannu". Shine nawa, jinkirtawa, gujewa wani abu wanda shine idan kai iya kokarinka zai kaika ga kusanta ga burukanka. Dukkan mu munayin haka, har Warren Buffett bai tsira ba shima. 

Cikin wasikar 1989 da ya aika ga masu rike da hannun jari kamfaninsa mai suna Berkshire Hathaway,  Buffett ya fadi cewa, "Na wuce wasu manyan sayayya wanda suka hidima a  faranti wanda nasami damar fahimta sosai. Amma ga masu hannun jari na Berkshire, hardani kaina, farashin da muka bayar na wannan tsotsar yatsa gaskiya babbane."

Babban darasi shine Ayadda duk wani hukunci mai mahimmanci na rayuwa, wanda ya hada da sanya hannun jari, kayi binkice ciki da bai, kasami dukkan bayanai, sannan kai wuff zuwa kan hukuncin da ka yanke. idan amsarka  a a ce, to kayi bayani budadde kamar yadda yake a ranka sannan ka ci gaba da tafiya da sanin cewa kayi zabin da ya dace

3. Kada kaiwa kanka alkalanci akan Daidain wasu Mutane

Photo by StuartMiles From Freerange Stock

Idan zaka saita gurbin cikar muradanka, kada ka sa kanka cikin tarkon auna nasarar wasu mutane. Maimakon gwada kanka da gama garin mutane, ka auna kanka akan gwadaban shararriyar dokar Buffett din nan ta -- Inner "Scorecard' Wanda shine ka maisaheda ma anar dai-dai da kanka ba yadda duniya ta bada ma ana ba.

Wannan ka ida ta inner "scorecard" tsarine dashi Buffett ya koya daga wajan mahaifinsa, hakan na nufin  abunda yake zuwa daga can kasan zuciyarka wanda kuma shine bayanin cikakkiyar gaskiyar ka. Kuma hakan nayima  bayani akan ma anar ko kai waye, da kuma yadda asalin halinka yake tareda yadda kake kallon duniya a mataki na ababen da kake girmamawa ko kai kai imani dasu, ba yadda wani yakeyi ba.

Ata kai ce irin wannan dayake fitowa daga rai yana iya kaika kololuwar hanyaar cimma nasara domin ya fito ne daga ranka. Idan har ka yadda da kanka toba shakka zakai nasara.


Idan ka Amfana kayi sharhi koda na fatan alkairine, karin haske ko kuma tambaya muna godiya..

Sanan za a iya turawa yan uwa abokai, masoya domin suma su karanata su amfana. Allah ya Datar Damu

Post a Comment